1/3
Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar screenshot 0
Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar screenshot 1
Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar screenshot 2
Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar Icon

Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar

first-rate-apps
Trustable Ranking Icon可信任
1K+下载次数
104MB大小
Android Version Icon4.1.x+
Android版本
2.9(16-02-2021)最新版本
-
(0 评价)
Age ratingPEGI-3
下载
详情评价版本信息
1/3

Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar介绍

Assalamu Alaikum


Wannan app yana dauke da Fassarar Sharhin Littafin Siffatus Salatin Nabiyyi Mp3 Offline na Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam, shine muka ga ya dace muyi application wanda mutane zasu su saurara a saukake.


Allah ya sakawa Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya kuma jikansa.


*Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam


An haifi marigayi SheikhJa'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakaninsu, wanda kuma shi nemu sabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.

Tunkafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar dasu, sun hada da tafsirin Alkur'ani, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy. Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre). Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa.

Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna.


Domin samun sauran apps na Sheikh Jafar da sauran manyan malamai na sunnah duba (first-rate-apps) free Hausa Islamic apps dake cikin play store


Don Allah idan har kaji dadin wannan application a taimaka a yi sharing ta facebook, whatsapp, twitter, da sauran social media domin sauran yan uwa musulmi su amfana.

Kada kuma a manta ayi rating na wannnan application five star.


Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar - 版本2.9

(16-02-2021)
其他版本
新特性1.This Update includes bug fixes and improvements2. New version with some awesome features

还没有评论或评分!要留下第一条评论或评分,请

-
0 Reviews
5
4
3
2
1

Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar - APK信息

APK版本: 2.9程序包: com.andromo.dev658544.app672243
Android兼容性: 4.1.x+ (Jelly Bean)
开发商:first-rate-apps隐私政策:https://rrnapps.blogspot.com/?m=1权限:7
名称: Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar大小: 104 MB下载次数: 12版本: 2.9发布日期: 2021-03-10 21:48:28最小屏幕: SMALL支持的CPU:
程序包ID: com.andromo.dev658544.app672243SHA1签名: E4:47:63:A6:69:EA:E7:06:12:1C:8F:C5:37:00:94:65:9A:31:0C:9B开发商 (CN): Andromo App组织 (O): "Andromo.com L本地 (L): 国家/地区 (C): CA州/市 (ST): MB程序包ID: com.andromo.dev658544.app672243SHA1签名: E4:47:63:A6:69:EA:E7:06:12:1C:8F:C5:37:00:94:65:9A:31:0C:9B开发商 (CN): Andromo App组织 (O): "Andromo.com L本地 (L): 国家/地区 (C): CA州/市 (ST): MB

Siffatus Salatun Nabiyyi Mp3 Part 1 - Sheikh Jafar的最新版本

2.9Trust Icon Versions
16/2/2021
12 下载次数104 MB 大小
下载

其他版本

2.8Trust Icon Versions
3/11/2020
12 下载次数104 MB 大小
下载